Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin siyasar Nijar Ka Iya Haifar Da Matsalar Ayyukan Jinkai


Wasu ‘yan gudun hijira
Wasu ‘yan gudun hijira

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, tayi gargadin cewa, rikicin siyasar kasar ka iya tabarbarewa har ya kai ga haifar da matsalar ayyukan jinkai, sakamakon ci gaba da haren da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi da kuma yadda radadin da takunkumin da ECOWAS ta kakabawa kasar ke fara tasiri.

Wakilin hukumar kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya a Kasar Nijar Emmanuel Gignac yace, tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaban zababbiyar Gwamnatin ta Nijar a ran 26 ga watan Yuli, kasar ta fada cikin rudani da rashin tabbas.

Yace, yana da wuya a san abinda zai iya faruwa, amma bisa la’akari da halin da ake ciki, hukumar kula da ayyukan jinkan da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, na wani shirin ko ta kwana domin tunkarar duk wani lamarin bazata da ka iya faruwa.

Gignac ya kara da cewa, tashe tashen hankula da hare haren kungiyoyi masu rike da makamai, musamman a kusa da kan iyakokin Mali da Burkina Faso sun daidaita mutane fiye da 20, 000 a watan daya gabata.

Ya kuma lura cewa, a daidai lokacin, ‘yan gudun hijira har 2,500, yawancin su daga Mali da Burkina Faso da wasu daga Najeriya sun tsero zuwa Nijar, lamarin da ya zafafa matsalar samun kariya ga ‘yan gudun hijirar, masu neman mafaka da masu masaukin su.

Hukumar tace, a halin yanzu Nijar na daukan nauyin mutane 700,000 da aka tilastawa rabuwa da matsugunnin su, rabin su ‘yan gudun hijira, rabin su masu neman mafaka, yayinda sauran rabin mutanen da aka raba da muhallin su ne a cikin gida.

A lokacin wata ziyara da ya kai zuwa Geneva, daga mazaunin shi a Yamai, Gignac ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa, matsayin Nijar na matsugunnin ‘yan gudun Hijira, na cikin mawuyacin hali.

Ya kara da cewa, Nijar hanya ce zuwa Arewacin Afrika, musamman Libya, sannan akwai masu neman mafaka, da mutanen dake da bukatar kariya daga duniya baki daya wadanda suka cakudu da ire iren wadannan tafiye tafiyen.

Amma saboda kan iyakokin na rufe, ba a sani ba ko malalar mutanen zata cigaba.

In ko har suka cigaba, yace, to lallai kuwa zasu faru ne ta boyayyar hanya matuka da tafi ta da, wanda hakan ka iya haifar da Karin cutar da mutane da cin zarafi.

~Hauwa Sheriff~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG