Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Siyasa A Jamhuriyyar Nijar Ya Dau Sabon Salo


A jamhuriyar Nijar wata kotun birnin Yamai ta bai wa shugaban rikon kwaryar jam’iyyar Moden Lumana Oumarou Noma, gaskiya bayan da ya shigar da karar shugaban jam’iyyar ta kasa Hama Amadou.

Oumarou Noma, dai ya zargi Hama Amadou ne da kwace masa hurumin shugabanci ba akan ka’ida ba. Sai dai magoya bayan babbar jam’iyar ta Adawa na cewa, wannan zai canza masu ra’ayi akan maganar takarar Hama Amadou a zaben 2021.

A farkon makon nan da muke ciki ne shugaban jam’iyyar Moden Lumana Hama Amadou, dake hijira a birnin cotonou, ya aike da wasika zuwa ga mataimakan sa, don sanarda su cewa ya damka ragamar jami’iyyar a hannunsu.

Sannan ya dakatar da shugaban rikon kwaryar jam’iyyar Oumarou Noma, daga mukaminsa, sai dai ya ce ba zai yi na'am da wannan mataki ba, mafari kenan daya garzaya kotu.

Bayan sauraren bangarorin, dangane da wannan karar, alkali ya baiwa Hama Amadou rashin gaskiya, saboda a cewarsa sashe na 8 na kundin zabe, ya haramta masa daukan kowane irin mataki da sunan jam’iyya sakamakon hukuncin da ya hau kansa.

Magoya bayan jam’iyyar ta Moden Lumana sun jaddada goyon baya ga jagoran na ‘yan Adawa Hama Amadou, saboda a cewarsu mutun ne mai akida.

Wannan rikicin shugabanci na kara karfafa ne, a wannan lokacin da ya rage mako 1 a gudanar da taron jam’iyyar na kasa da zai tabbatar da sunan wanda zai tsaya mata a zaben shugaban kasa na 2021.

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar Moden Lumana Oumarou Noma, yace lokacin magana bai yi ba.

Da yammacin Juma’ar yau ne jiga-jigan jam’iyyar ta ‘yan Adawa ke gudanar da taro domin tattauna hanyoyin da zasu bi don dai-daita wannan lamarin.

A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG