Duniya na mayar da martani ga mummuna ko kyakkyawan tasirin da yakin ke yi, yayin da abin ke shafar farashin wasu kayayyakin, wadanda ko dai Rasha ko Ukraine ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya.
Rasha da Ukraine sun shahara wajen fitar da albarkatun man fetur, alkama da sauran kayayyaki masu alaka, don haka yakin da ke tsakaninsu ya yi sanadin tashin gwauron zabi na farashin wadannan kayayyaki a duniya.
Masu sharhi sun ce, kasashen Afirka su ma ba su tsira ba a wannan fanni.
A zantawarsa da wakilin Muryar Amurka a Kano-Nigeria, shugaban kungiyar manoman alkama a Najeriya, Dr Salim Sale Muhammad, ya ce farashin kayayyakinsu ya yi tashin gwauron zabi biyo bayan mamayar da Rasha ta yi a kasar Ukraine, kuma rikicin ya kara farashin kayan aikin noma da kayan masarufi, galibinsu wanda ake shigo da su cikin ƙasar.
Kasancewar Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur, Najeriya na cin gajiyar tsadar farashin danyen mai a kasuwannin duniya sakamakon yakin da Rasha ta ke yi a kasar Ukraine, in ji Dokta Lawan Habib Yahaya, masani kan harkokin tattalin arziki a Kwalejin Kimiyya da Fasaha (Polytechnic) ta jihar Kano.
Sai dai ya shaida wa manema labarai cewa, karin farashin ba zai yi wani tasiri mai kyau ba ga rayuwar ‘yan Najeriya saboda tsadar sayowa da tace man fetur a cikin kasar da kuma hauhawar farashin canji da faduwar darajar Naira.
Ya kuma bayyana cewa, kalubalen tsaro na iya zama cikas ga Najeriya wajen samun ribar yakin ta hanyar samar da kayayyakin amfanin gona ga sauran kasashe domin manoma da dama na shakkun zuwa gona.
A farkon rikice-rikicen dai, rahotanin sun ce ministan kudin Najeriyar ta bayyana cewa, yuwuwar kudaden shigar da ake samu daga hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya, za a yi amfani da su ne wajen biyan basussukan da Najeriya ta ciwo, don haka ‘yan kasar za su kasa ganin amfani ko tasirin kai tsaye.
An bayar da rahoton cewa, kasar Ukraine na samar da kashi 34% na alkamar da Najeriya ke amfani da ita a duk shekara, don haka dole ne Najeriya ta maida hankali cikin gidanta don cike gibin da rikicin Rasha da Ukraine ya haifar a watan Fabrairun bana.