Muhammed Barde Agwai shugaban matasa na jam'iyyar a jihar ya bayyana dalilan da suka sa 'yan jam'iyyar na jihar suka gudanar da gangamin.
Yace sun gudanar da gangamin ne akan su nuna goyon bayansu ga 'yanuwansu 'yan majalisa domin suna aikinsu cikin ka'ida amma gwamnati tana anfani da wasu mutane domin a ci mutuncinsu. Gwamnatin tana nunawa kamar 'yan majalisan basu da goyon bayan jama'a. Burinsu shi ne su nunawa duniya cewa jihar ta PDP ce.
To amma 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar sun mayar da martani. Alhaji Abdulkarin Allah Nananan daga Keana shugaban matasan jam'iyyar yace gangamin PDP tamkar rashin sanin doka ne. Yakamata su koma makaranta su sake karanta kundun tsarin mulkin kasar. Lokacin gangamin ma wai 'yansanda sun fi jama'a yawa.
Magoya bayan jam'iyyun sun bayyana nasu ra'ayoyin. Alhaji Nasiru shugaban PDP na karamar hukumar Lafiya yace ganin cewa 'yan majalisa na aikinsu cikin ka'ida yasa 'yan APC suka nuna damuwarsu. Wai sun fito ne su nunawa mutane cewa 'yan majalisa suna da mutane kuma babu wanda ya isa ya razanasu. Amma Hajiya Rakiya shugabar matan APC ta jihar tace gangamin nasu borin kunya ne. Dimokradiya ce. Kowa yana da 'yancin yayi abun da ya ga dama. Babu ma wanda ya san sun yi gangamin domin su 'yan majalisar ma ba zasu iya dawowa jihar ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.