Shugaban bangaren jam'iyyar CDS Rahama mai ra'ayin kawo sauyi, Malam Abdu Labo ya ce lallai kam ya wajaba a yi babban taro na "congre" kamar yadda gwamnati ta ce. Ya ce muddun jam'iyyarsu ta CDS ba ta yi babban taro na "congre" ba to za ta fuskanci rusarwa daga gwamnati. Abdu Labo ya ce duk wanda bai so a yi babban taro na "congre" to bai son cigaban jam'iyya. Don haka, in ji shi, Mahamman Usuman ba ya son cigaban CDS Rahama.
To saidai kuma da wakilinmu Abdullahi mamman Ahmadu ya tuntubi kakakin bangaren su Mahamman Usuman mai suna Dodo Rahman sai ya ce sam Abdu Labo bai da ikon kiran babban taro na "congre." Ya ce ana amfani ne kawai da su Abdu Labon don a yi zagon kasa ma jam'iyyar CDS Rahama.
Da wakilinmu ya tuntubi shugaban kungiyar masana kundin tsarin mulkin Janhufriyar Nijar, Dr. Ahmadu Bakari sai ya ce lallai muddun jam'iyyar ta kasa gudanar da babban taro na "congre" cikin wa'adi to ana iya rusa ta. To amma al'amarin CDS ya banbanta saboda ya shafi rigimar cikin gida wadda har ta kai ga kotu.