Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Za Ta Yi Amfani Da Karfin Tsiya Kan Kungiyoyin Kurdawa


Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi ta nanata cewa za a yi amfani da karfin tsiya wajen kawar da kungiyoyin Kurdawa na YPG da PKK a Siriya da Iraki.

"Ba mu banbanta kungiyoyin ta'addanci irinsu Daesh da YPG da al-Qaida da sauransu - dukkansu daya ne a wurinmu," a cewar Erdogan ranar Laraba a wani taron manema labarai tare da takwaran aikinsa na Rasha Vladamir Putin, a birnin shakatawar nan na Sochi da ke gabar tekun Black Sea.

Erdogan ya ce sojojin kasar za su cigaba da daukar matakan soji a tsawon kan iyakar kasar da ke kudu. "Gwadda su kasance cikin tsoro a maimakon mu yi ta damuwa game da harin 'yan ta'adda," a cewar Erdogan ranar Lahadi, ya na mai gargadin yiwuwar sojojinsa su ketare kan iyaka su kai hari.

Jiragen yakin Turkiyya samfurin jet sun kai hari kan yankin Sinjar na Iraki a watan jiya, inda su ka auna mayakan Kurdawan kasar Siriya na YPG da PKK.

Turkiyya na ganin YPG wani bangare ne na PKK, wadda ke yaki da gwamnatin Turkiyya kan saboda a bayar da karin hakkoki ga tsiraru, kuma Amurka da Turai sun ayyana ta a zaman kungiyar ta'addanci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG