Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Sojan Amurka A Somaliya


Mayakan Al-Shabaab
Mayakan Al-Shabaab

An kashe wani sojan Amurka a lokacin wata bata-kashi da aka yi tsakanin sojan Amurka din da mayakan kungiyar al-Shebab a can Somaliya.

A yau Jumu’a ne rundunar sojan ta Amurka ta tabattarda cewa an kashe mata wannan sojan a kusa da garin Barii wanda tazarar kilomita 40 ta raba shi da Mogadishu, babban birnin kasar.

Haka kuma rundunar sojan Amurka din dake nahiyar Afrika tace wannan al’amarin ya faru ne a lokacinda sojanta ke aiki tareda na Somalia wajen jan daga da su mayakan na al-Shebab.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG