Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Dubu 37 Ke Gudun Hijira a Jamhuriyar Nijar


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima
Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

Rigingimun da kungiyar Boko Haram ke haddasawa a jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun sa dubban mutane sun fantsama cikin wasu garuruwa har da na kasashen dake makwaftaka da Najeriya

Kawo yanzu an yi kiyasin cewa kimanin 'yan Najeriya dubu talatin da bakwai ne ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar kadai banda wasu kasashen kamar Kamaru da Chadi.

Ganin yadda wannan matsalar ke kara yaduwa ya sa aka samu karin 'yan gudun hijira. Lamarin da ya sa gwamnatin jihar Borno kafa kwamitoci a matakai daban daban domin kaiwa al'ummarta da suka fada cikin halin kakanikayi doki a duk inda suke har da kasashen wajen.

Alhaji Abubakar Kyari shugaban ma'aikata a fadar gwamnan Borno wanda kuma yake shugabantar daya daga cikin kwamitocin sun yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar domin kai kayan agaji ga al'ummar jihar. Alhaji Abubakar ya yaba da irin tanadin da gwamnatin Nijar tayi tare da hukumar majalisar dinkin duniya da wasu kungiyoyi.

'Yan Borno dake Jamhuriyar Nijar suna cikin wani halin dake bada tausayi domin da kyar a samu iyalai da suke tare da 'yanuwansu. Yace za'a samu mace da bata san inda mijinta yake ba ko kuma yara da basu san inda iyayensu suke ba. Za'a ga yaro dan shekara takwas ko kasa da haka bai san inda iyayensa ko sauran 'yanuwansa suke ba. Wasu kuma da yawa sun rasu cikin ruwa domin kwalekwalensu da ya kife cikin kogi. Wasu ma a waje suke kwana. Wasu kuma basu da komi sai rigunan jikinsu.

Kungiyoyi dake zaman kansu suna kawo nasu dokin. Alhaji Sagir Abdullahi shugaban 'yan gwanjon jihar Borno sun kai nasu doki tun daga wadanda suke cikin garin Maiduguri. Ya kira duk masu hali a Najeriya su tashi su taimaki wadanda suka tagayyara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG