WASHINGTON, DC —
Tsige Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna Alhaji Muazu Usman Gangara da Mataimakin Mr Dogara Mato da wasu ‘yan Majalisar su ka yi ikirarin yi ranar Talata ya dau wani sabon salo, ta yadda Kakakin da aka ce an tsigen ya ce har yanzu ya na nan daram dakau a mukaminsa.
A wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, Alhaji Gangara ya ce hatta zaman da ‘yan Majalisar su ka yi na tsige shin haramtacce ne, sannan bugu da kari ‘Yan Majalisar ba su kai adadin da doka ta ce ba. Wakilinmu a Kaduna Isah Lawal Ikara ya ruwaito Alhaji Gangara na jaddada cewa masu ikirarin tsige shin ba su da sulusi biyu (2/3) da ake bukata.
To amma sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Shehu Usman Tahir tuni ya rusa dukkan kwamitocin Majalisar da zummar kafa sabbi nan gaba. To saidai wakilinmu ya ruwaito shi ya na alkawarin hada kai da kowani dan Majalisar da ma’aikatanta .
Game da zargin cewa an bai wa ‘yan Majalisar da su ke ikirarin tsige Kakakin cin hanci kuwa, wani tsohon Kakakin Majalisar kuma dan Majalisar a yanzu mai suna Alhaji Jumare Hassan Buranco ya rantse cewa babu wanda ya ba su cin hanci don su tsige Kakakin Majalisar. Ya ce sun yi don radin kansu.