A cikin firar tasu ministan ya ce ba China kadai suke muamala ba har da Ingila da wasu kasashen domin kara gina birnin Abuja. Ya ce ganin haka ya sa Amurka ta yi sha'awar shigowa. Yanzu zasu taimaki birinin da gyara yanayi da gina muhallai musamman na masu karamin karfi wajen matsuguni da kuma gidaje.
Akwai wani shiri kuma na musayar fili. Wannan in ji ministan shiri ne wanda za'a baiwa masu arziki katafaren fili su sa ma'adanai kamar hanyoyi, wutar lantarki da ruwa da dai makamantansu ya kasance da mutum ya zo kawai sai dai ya gina filinsa ya shiga. Daga filin wadanda suka saka ma'adanan zasu dauki kashi 60 kana gwamnati ta bayar da sauran kashi 40 wanda z'a baiwa marasa karfi wato talakawa da sauran ma'aikata. Filayen za'a gina gidaje da makarantu da asibitoci da wuraren kasuwanci.
Dama a cikin tsarin Abuja gundumomi 83 za'a gina. Amma kawo yanzu duk da girman kashi goma sha daya kawai aka gina. Amma yanzu da taimakon manyan 'yan kasuwa goma sha biyar za'a kara gina gudumomi goma sha daya.
Ga karin bayani.