Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Babban Bankin Najeriya Na Takaita Fitar Da Kudade Daga Banki


Kudin Najeriya
Kudin Najeriya

‘Yan kasuwa sun koka dangane da sabon tsarin da babban bankin Najeriya ya ke shirye-shiryen fitowa dashi, na takaita fitar da kudade da cakin banki iya Naira Dubu Goma, ya yin da masana tattalin arziki da hada hadar bankuna a kasar su kace matakin ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ba tayi bitar yanayin ba kafin fara aiwatar da tsarin a wasu jihohin kasar.

Kimanin shekaru 4 da suka gabata ne babban bankin Najeirya CBN ya bullo da sabon tsarin takaita ta’ammali da takardun kudade tsakanin ‘yan kasar, kuma ya mayar da gurbinsa da amfani da kafofin sadarwa musamman na internet wajen gudanar da cinikayya tsakanin al’umma.

Yanzu haka dai babban Bankin na nan zai fito da wata doka dake haramta cire kudi da suka wuce Naira dubu Goma, daga Banki ta hanyar amfani da cakin kudi.

A cewar Alhaji Yusuf Musa Dorayi, wani dan kasuwa dake mu’amula da kananan ‘yan kasuwa, yace kananan ‘yan kasuwa da mutanen kauyen da basa amfani da banki ta yaya za a iya kasuwanci da su idan aka hana fitar da kudi kamar yadda aka saba.

Shi kuwa Alhaji Sharo Uba, na mai ra’ayin cewa matakin da na iya jefa al’umma cikin hadarin yawaitar fashi da makami.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG