Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwa Da Burin Mawaki Attah Charles


Nas T. Breed Nasarawa
Nas T. Breed Nasarawa

Yau a filin Nishadi wakiliyar DandalinVOA ya samu hira da Attah Charles wanda aka fi sani da Nas T Breed Nassarawa, Top Breed kauran rappers na jihar Nassarawa.

Nas mawakin hip hop ne wato gambara, ya fara waka ne shekaru takwas da suka wuce, kuma babban jigonsa a harka ta waka shi ne mahaifinsa sakamakon yawan sauraren wakokin da yakan yi .

Ya kara da cewa mahaifinsa ya ba shi goyon baya wajen yin waka, dalilin da bai samu korafi ba, ko da ya ke ya ce bai samu goyon baya daga wajen sauran mawaka ba, amma ya samu goyon baya daga wajen dan uwansa wanda ya taimaka masa har ya kawo yanzu.

Ya ce waka wata hanya ce ta nishadantarwa a hannu guda, kuma wata dama ce ta nemar wa kansa, wato abin dogaro da kai.

Ya ce ko ba komai, dan uwansa ya taimaka masa matuka, mussamam ma wajen hada masa sauti da duk wani goyon bayan da ya bukata domin cimma burinsa.

Ya ce babban burinsa shi ne ya zama babban mawaki, ya kuma taimakawa kananan mawaka masu tasowa.

Ga cikakkiyar hirarsu da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG