Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Wutar Lantarki Yana Barazana Ga Tattalin Arzikin Zimbabwe


Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa

Kasar Zimbabwe tana husakantar karancin wutar lantarki mafi muni a ‘yan shekarun nan, lamarin da ya kai ga ma’aikata suka koma aikin dare, lokaci kadai da ake samun wutar lantarki.

Gwamnati kasar tana dora laifin karancin wutar lantarkin ne a kan kasuwanni da masana’antu da basu biyan kudin wuta.

Kamar kowane bangaren kasar, babban birnin kasar Harare tana samun wuta na awa bakwai ne a kowace ranar a cikin dare.

Karancin wutar da Zimbabwe ke huskanta shine mafi muni a cikin shekaru uku, masu fashin baki sun ce wannan lamari yasa kasar na asarar miliyoyin daloli daga ayyukan yau da kullum.

Duk da cewa akwai injin janarato da dama, amma karancin man fetir da Zimbabwe ke fama da shi ya sa ba a iya amfanin da injinan.

Zimbabwe tana tattaunawa da kasashen Mozambique da Afrika ta Kudu domin taimaka mata da kwararru na fanin wuta kuma Harare tana sa ran tattaunawar zata yi tasiri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG