A kasar Libya, fyade da kisan kai da kuma garkuwa da mutane abu ne da aka saba gani, wanda yake da wahala a sami wani da bai taba fuskantar irin wadannan abubuwa ba. Tun kafin shiga irin wannan hali, mutanen da suka guje wa yaki da kisan kare dangi da tashe-tashen hankula na ‘yan daba da kuma talauci, sun bar gida ne saboda su na son su rayu.
Libya dai tamkar wani zango ne da ke dab da Turai, kuma yawancin wadanda suka tsira da ransu akan hanyarsu ta niyyar zuwa Turai, sau tari su kan yi fatan za su kai har zuwa Turan.
Kafin nan, su kan fada cikin wahalar kame, da rashin matsugunai, da yaki da kuma talauci. Su na cike da tsoro, a cewar bakin hauren.
Facebook Forum