Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Yi Bincike Kan Matsalar Katsewar Wutar Lantarki


Zauren Majalisar wakilan Najeriya
Zauren Majalisar wakilan Najeriya

Ya kara da cewa a jimullance, sau takwas tushen wutar na kasa yake rugujewa a shekarar 2024.

Majalisar Wakilain Najeriya ta umarci kwamitinta kan harkokin wutar lantarki da ya binciki yawan matsalar katsewar tushen wutar lantarki na kasa sannan ya gabatar da rahoto cikin makonni uku.

Cikin mako guda, wutar lantarki ta katse akalla sau uku a duk fadin kasar yayin da ta katse sau hudu a wasu yankuna.

Wannan mataki ya biyo bayan kudurin gaggawa na kasa da Hon. Mansur Manu Soro (Bauchi, PDP) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

A cikin kudurinsa, Soro ya nuna matukar damuwa kan yawan rushewar tushen wutar, wanda ya jefa kasa baki daya cikin duhu, ya kara tsananta matsalolin tattalin arziki da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Ya jaddada cewa samar da wutar lantarki mai dorewa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kowace kasa.

Ya kara da cewa a jimullance, sau takwas tushen wutar na kasa yake ruguje a shekarar 2024.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG