Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun UNICEF Ya Sami Tallafi Daga Kungiyar Tarayyar Turai Na Tsabtace Muhalli A Nigeriya


UNICEF
UNICEF

Kungiyar Tarrayar Turai ba asusun tallafawa kanananan yara- UNICEF naira biliyan tara domin kula da harkokin lafiya, ruwa da tsabtace muhalli a jihohin Plateau, Ekiti, Adamawa da kuma Kebbi.

Kungiyar Tarrayar Turai ba asusun tallafawa kanananan yara- UNICEF naira biliyan tara domin kula da harkokin lafiya, ruwa da tsabtace muhalli a jihohin Plateau, Ekiti, Adamawa da kuma Kebbi.

Jami’in sadarwa na asusun tallafawa kananan yaran a Najeriya Mr Geoffrey Njoku ne ya bayyana haka. Bisa ga cewarshi, an sa hannu a takardar yarjejeniyar gudanar da aiki na tsawon shekara biyar da nufin taimakon kauyuka domin cigabansu.
Mr. Njoku ya bayyana cewa, Jihohin jihohin Plateau, Ekiti da Adamawa zasu sami kimanin naira biliyan, a kuma ci gaba da taimakonsu na tsawon shekaru hudu inda za a kashe wani kudi kimanin naira biliyan N6.75.

Za a yi amfani da wadannan kudaden ne wajen taimakon mata masu ciki, jarirai da kula da lafiyar kananan yara a jihar Kebbi da Adamawa.

Jami’in asusun UNICEF ya bayyana cewa, za a gudanar da ayyukan ne bisa yarjejeniyar da aka sa hannu ranar 30 ga watan Afrilu, 2013 tsakanin gwamnatin Nigeriya da kungiyar Tarayyar Turai (EU), domin karfafa ci gaban da ake samu a kasashen.

Njoku, yace wannan shiri na tanajin ruwa da tsabtace muhalli da birane, yana karkashin rukunin shirin na uku a karkashin shirin da ake kira “WSSSRP III” wanda UNICEF take aiwatarwa, da nufin samar da ruwan sha a kauyukan Jihohin Adamawa, Plateau da Ekiti.

Kimanin kananan yara 2,100 kasa da shekaru biyar da mata masu ciki 75 suke mutuwa kowacce rana a Nigeriya, daga cututtukan da za’a iya karewa da suka hada da cututtuka kamar cizon sauro, ciwon hakarkari da gudawa.

Kashi 10% na mata masu ciki da suke mutuwa a duniya suna mutuwa ne a Nigeriya. Yayinda kusan kashi 24% na kananan yara kasa da shekara biyar basu da nauyi yadda ya kamata kashi 36% kuma basu girma yadda ya kamata

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG