Shari'ar dai ta dauki hankalin jama'a sobada ana ganin kamar ana sako sako da lamarin musamman duba da fitowar da aka yi kotu a baya wadda ba a yi zaman shari'ar ba.
Labarin Fatima Sulaiman daliba ‘yar shekara 16 da ta rasa kafarta sanadiyyar bige ta da mota da Aliyu Sanusi Umar ya yi, lokacin da suke murnar kammala jarabawar NECO, ba bakon abu bane ga duk mai amfani da kafar sa da zumunta ta facebook.
Fatima Sulaiman ta ce yaron ba dan makarantar su bane kuma daga farko sai da aka kore shi da ya shigo makarantar inda daliban ke wasan murnar kammala jarabawa.
Ta ce bayan an tashi makarantar sun fito waje sai yaran dake wasan suka dauko motoci suna wasa.
A cewar ta su kuma suna zaune su uku suna jiran a zo daukar su sai motar ta nufo wurin da suke zaune, biyu daga cikin daliban da ke zaune suka gudu ita ma ta yunkura ta gudu sai ta fadi motar ta same ta, tace tana neman ayi mata adalci ga halin da ta samu kanta ciki.
Bayan da jama'a suka yi ta yada hotonan wata fitowa kotun da aka gurfanar da yaron wadanda suke cike da shakku, yanzu dai kotun ta zauna cikin tsattsauran tsaro inda aka tuhumi yaron da laifuka uku da suka hada da tukin mota ba tare da lasisi ba, tukin ganganci da kuma yin sanadin samuwar mummunan rauni.
A zaman kotun dai lauya mai kare wanda ake zargi, Jacob Ochidi SAN, ya nemi bukatar bayar da yaron beli domin a cewarsa laifukan da ake tuhumarsa ba manyan laifukan da ba'a bayar beli bane.
“Doka tace ana bayar da beli ga laifukan da ba manyan laifuka sai in akwai wasu kwararan dalilai na kin bayar da shi, to a wannan shara'ar babu dalilan da kan iya hana a bayar da shi beli, muna tausaya wa yarinyar da iyayenta akan yanayin da suka shiga, dukan mu ‘yan Adam muke abinda ya faru abin tausayi ne don haka muke tausaya wa iyayenta"
Sai dai lauyan masu shigar da kara, Jamilu Malami, ya kalubakanci wannan bukatar .
Wakilin sashen Hausa ya zanta da lauyan bangaren yarinyar da aka ji wa mummunan rauni, Muhammad Mansur Aliyu, akan zaman kotun. Ya ce, "lauyoyin yaron sun shigar da bukatar beli amma dai bangaren gwamnati da bangaren yarinyar sun ki aminta, domin sun samu wani bayanin sirri cewa yaron ya samu gurbin karatu a kasar waje don haka akwai yuwuwar zai iya barin kasar nan kowane lokaci, sannan kuma akwai yuwuwar cewa ko don lafiyar shi ya kamata a bar shi gidan gyaran hali har kura ta kwanta."
Alkalin kotun majistire, Mariya Haruna Dogon Daji, ta daga zaman zuwa 8 ga wannan wata don yanke hukunci akan bayar da belin ko akasin haka.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir: