Rashin jituwa ta barke tsakanin shugabannin kamfanonin Facebook, da na manhajar Whatsapp, kamfanonin biyu sun hau teburin munki wanda suke neman barin makudan kudade a tsakanin su da suka kai damar Amurka billiyan $1.3.
Takaddamar ta taso ne a dai-dai lokacin da kamfanin Whatsapp yake kokarin fito da wasu hanyoyi da zai dinga shigar da tallace-tallace a kan manhajar, wanda kamfanin Facebook, kuwa yake ganin hakan bai kamata ba, domin kuwa kamfanin na Facebook, na samun kudaden shiga ta hanyoyin talla da yake sakawa a shafinsa.
Shi kuwa kamfanin na Whatsapp, ya tabbatar da cewar bayan samun kudaden shiga ta ko ina, ya dogara ne daga kudaden da babban kamfanin na Facebook ke bashi, son haka shugaban kamfanin yake ganin cewar, akwai bukatar su dinga fitar da tallace-tallace a manhajar. Hakan dai ya kawo babbar takaddama tsakanin kamfanonin biyu.
Facebook Forum