Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Yin Mummunar Gasar Cinakayya Tsakanin Amurka Da China Na Karuwa


President Donald Trump speaks during a roundtable discussion on tax policy Thursday, April 5, 2018, in White Sulphur Springs, W.Va.
President Donald Trump speaks during a roundtable discussion on tax policy Thursday, April 5, 2018, in White Sulphur Springs, W.Va.

Amurka da China, jiga-jigai a fagen kasuwanci, na barazanar shiga mummunar gasar cinakayya da juna. Tuni su ka shiga saka haraji kan kayakin da kowannensu ke kaiwa kasashen juna.

Cacar baka irin ta gasar cinakayya ta dada tsanani tsakanin Amurka da China zuwa yau dinnan Jumma’a, inda Shugaba Donald Trump ya yi barazanar saka karin haraji na dala biliyan 100 kan kayan da China ke shigo da su Amurka, yayin da ita kuma China ta yi gargadin cewa za ta ja da Amurka ko ta halin kaka.

Jiya Alhamis Trump y ace ya umurci wakilan Amurka a bangaren cinakayya da su dubi yiwuwar kara haraji ma China bayan da Chinar ta fitar da jerin sunayen kayakin da Amurka ke kaiwa Chinar, ciki har da waken soya da kananan jiragen sama, wadanda kudinsu ya kai dala biliyan 50 da cewa su ma za ta saka masu karin haraji. Tun da farko a wannan satin Amurka ta saka haraji kan kayakin China da kudinsu ya kai dala biliyan 50.

A wata takardar sanarwa ta yau dinnan Jumma’a, Ma’aikatar Chinakayyar China ta ce muddun Amurka ta dau matakin abin da Chinar ta kira kare kasuwarta, to China za ta “jajirce har zuwa karshen al’amarin ko ana ha maza ana ha mata, kuma labudda za ta rama sosai.”

Farashin hannayen jarin Amurka ya fadi bayan da Trump ya bayar da umurni na baya-bayan nan kan cinakayya. Darajar Dow ta fadi da maki wajen 400 a cinakayyar karshe.

“A maimakon China ta gyara kuskurenta, ta zabi yin illa ga manomanmu da masu masana’antunmu,” a cewar Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG