Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce tilas ma'aikatan diplomasiyar Amurka 755 su fice daga cikin kasarsa a wani mataki na mayar da martani a kan sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa Rashan saboda kutse da ake zargin ta yi a zaben 2016 domin taimakawa shugaba Donald Trump ya lashe zaben.
Putin ya shaidawa talbijin din kasar cewa sama da mutane 1000 suke aiki a ofishin jakandanci da wasu ofisoshin diplomasiyar Amurkan, kuma ya ce tilas 755 daga cikin su, su dakatar da ayyukansu a cikin Rasha.
Shugaban na Rasha ya ce akwai yiwuwar Moscow ta kara daukar matakan martani a kan Amurka biyo bayan aminecwar bai daya da majalisun kasar ta yi wurin kakabawa Rasha sabbin takunkumi.
Tun da farko, mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya fadawa labaran telbijin ABC cewar sun yi jinkiri wurin daukar wannan mataki.
Facebook Forum