Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mata Ta Duniya: Yadda Mata A Kamaru Su Ka Yi Bikin Ranar


Kasuwa a birnin Yaounde na kasar Kamaru
Kasuwa a birnin Yaounde na kasar Kamaru

A ranar Mata ta duniya dubban mata sun fita kan tituna a kasar Kamaru don nuna adawa da tsadar rayuwa. Sai dai gwamnati ta dora alhakin hauhawar farashin kayan abinci da makamashi kan mamayar da Rasha take a Ukraine.

Daruruwan mata a Kamaru sun fita kan tituna suna busa kakaki a kan titunan babban birnin kasar Yaounde, da ke tsakiyar Afirka, suna kururuwa da kuma kokawa kan tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Matan sun ce suna son gwamnati ta taimaka musu wajen shawo kan hauhawar farashin da tsadar rayuwa.

Suzanne Menanga ita ce kodinetar wata kungiyar mata a Kamaru, wadda ta shirya zanga-zangar.

Ta ce kungiyar ta ta yi zanga-zangar ne a ranar mata ta duniya, saboda sama da kashi 80 cikin 100 na mata miliyan 14 na Kamaru ba su da aikin yi, ko kuma suna samun karancin albashi wanda ke da wahala a iya fuskantar tsadar rayuwa.

Ta ce karin albashi mafi karanci a watan Fabrairun 2023 ga ma’aikata masu dogaro da kansu daga kusan dala 60 zuwa dala 68 da karin kashi 5.4 na albashin ma’aikatan gwamnati bai inganta rayuwar 'yan Kamaru ba.

Menanga ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya karu daga kashi 25 cikin 100 a shekarar 2022 zuwa kashi 40 cikin 100 a shekarar 2023, inda ta ce da wuya iyalai su iya sayen kayayyakin da ake bukata kamar burodi da sukari da kifi da gishiri da sabulu da kayan lambu, wadanda farashinsu ya tashi daga tsakanin kasha 18 zuwa 45.

Matan sun ce ya kamata a kara mafi karancin albashin ma’aikata masu dogaro da kansu zuwa akalla dala 100. Ya kamata gwamnati ta kara albashin ma’aikatan kasar da kashi 20 cikin 100, a cewar matan.

Gwamnati ta ce an gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama da suka hada da Bamenda da Bafoussm da Ngaoudere da kuma Ebolowa a ranar Laraba.

Luc Magloire Mbarga Atangana shi ne ministan kasuwanci na Kamaru. Ya ce yakin da Rasha ke yi a Ukraine ya haifar da karin farashin kayayyakin masarufi a duk fadin duniya.

Atangana ya ce ya kamata fararen hula su koyi rayuwa tare da karin farashin. Ya kara da cewa yanayin rayuwa yana shafar duk fadin Afirka kuma yana iya ragewa ne kawai idan Rasha ta daina ta'addanci a Ukraine.

A shekarar da ta gabata gwamnatin Kamaru ta ce shugaba Paul Biya, ya ba da umarnin a gaggauta fitar da sama da dala miliyan 15 domin noman alkama da shinkafa a kasar da ke tsakiyar Afirka.

Gwamnati ta bukaci fararen hula da su ci abincin da ake samarwa a cikin gida maimakon shigo da su daga kasashen waje.

Matan sun ce da wuya su bi umarnin gwamnati na hana dogaro da shinkafa da masara da wake masu tsada, da ake shigo da su daga kasashen waje saboda karuwar farashin taki da kashi 60 cikin 100 ya kawo wahalar noman amfanin gona a cikin gida.

Ma'aikatar noma ta ce tuni ta kashe dala miliyan daya kan tallafin taki, tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a watan Fabrairun bara.

Ranar mata ta duniya, ta kunshi murnar nasarorin zamantakewa da tattalin arziki da al'adu da siyasa da mata suka samu. Hakanan kuma rana ce ta kira zuwa ga habaka daidaiton jinsi.

Wakilin Muryar Amurka a Kamaru, Moki Edwin Kindzeka shine ya hada wannan rahotan.

XS
SM
MD
LG