Bisa ga shirin majalisar dinkin duniya an gudanar da taron hakuri da juna a Gombe babban birnin jihar Gomben Najeriya. Manufar taron shi ne fadakar da alumma domin nuna hakuri da jumriya da juna ko menene ma banbancen dake tsakaninsu, da fahimtar da juna da kuma inganta matsayin dan adam. Taron kuma na bayyana yadda za'a kare hakin jama'a, mutuntawa da kuma hada kan kabilu daban daban da kuma addinai daban daban.
A jihar Gombe an gudanar da irin wannan taron. Barrister Abdulhamid Ibrahim Kwamishanan shari'a na Gombe ya bada kasida a wurin taron. Ya ce majalisar dinkin duniya ta tsayar da ranar a matsayin ranar hakuri ta duniya. Hakuri kuma yana da mahimmanci a rayuwar bil adama. Ya ce yana kara tunawa mutane anfanin hakuri da kuma abun da hakuri zai haifar da kuma gudun abun da rashin hakuri zai haifar. Yana fata al'ummar Gombe sun fahinceshi a kan a dagewa a yi hakuri da juna.
Kwamishana Ibrahim ya ce akwai hanyoyi da yawa na neman haki.Akwai kotuna. Idan kana ji an taka maka haki ka je kotu ka shigar da kara. Ana iya fara shari'a daga kotu karama har a kai kotun koli na kasa. Mutane basu da hakuri ne kawai domin idan mutum ya bi fannin shari'a zai wayi gari ya ga an bashi hakinsa.
Wasu da suka halarci taron sun ce tabbas babu shakka idan an rungumi akidar zaman lafiya za'a cigaba da samun nasara domin sau da yawa duk wasu rigingimu dake faruwa jama'a suke haddasasu sanadiyar rashin hakuri.Sun ce kamata ya yi mutane su guje ma manyan 'yan siyasa masu son yin wasa da hankulan jama'a. Irin wannan taron ya kamata a yi shi a kowane gari domin hakuri nada mahimmanci wurin kawo zaman lafiya.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.