Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Nijar


Litattafai da harshen Hausa
Litattafai da harshen Hausa

Kungiyoyin bunkasa harshen Hausa da al’adun Bahaushe a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da bikin tunawa da ranar Hausa ta duniya kamar yadda bikin ke gudana a kasashen Hausa a wannan Litinin 26 ga watan Agusta.

Yanayin tsaron da ake ciki a Nijar da makwabta ya sa hukumomi da wadannan kungiyoyin karkatar da akalar shagulgulan wannan rana kan gudunmowar da harshen Hausa ke bayarwa a ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Dakin taro na cibiyar raya al’adu CCOG na birnin Yamai a wannan Litinin ya samu dandazon jama'a domin bikin ranar Hausa ta duniya wacce ta samo asali a 2015 bayan da wani dan Najeriya Abdulbaki Jari ya yi kiran masu amfani da kafar sadarwar Twitter su rika rubuce-rubucensu da harsunan Hausa don bunkasa harshen ta wannan hanya.

Litattafan Hausa
Litattafan Hausa

Ranar wacce ke kara samun karbuwa ta zama wata damar tattauna matsalolin al’umma sabili kenan aka ta'allakar da bikin na bana kan gudunmowar harshen Hausa a sha’anin wanzar da zaman lafiya.

Yayin da alkalumma suka nuna cewa Najeriya na da Hausawa kusan million 60 an gano cewa kashi kusan 60% na jama’ar Nijar mai mutane million 27 suna jin Hausa abinda ke fayyace matsayin Harshen a ayyukan fadakar da jama’a ta wannan dalilin neman gwamnatin Nijar ta tashi haikan da yunkurin shimfida tsarin karatu da harsunan gida a makarantun boko kamar yadda ministan ilimi da bunkasa harsunan gida Dr. Elizabeth Cherif ta bayyana.

Gamayyar kuniyoyin kare hakkin mata da yara wato CONGAFEN ta jaddada aniyar ba da gudunmawar da za ta taimaka a cimma gurin da aka sa gaba a karkashin taken ranar ta bana inji shugabarsu Mme Kako Hajiya Fatima.

Litattafan harshen Hausa
Litattafan harshen Hausa

An yi amfani da wannan dama don jajantawa al’ummar Hausawan duniya rasuwar Sarkin Sabon Birni ta Najeriya wanda ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla bayan shafe makwanni suna garkuwa da shi da sunan neman kudin fansa. Dattawa irinsu tsohon shugaban majalissar jihar Zinder Alhaji Moutari Ousman sun yi kira a kai zuciya nesa a duk lokacin da irin haka ta faru.

An kuma gayyato masana kan tarihi da al’adun Hausa da za su gabatar da laccoci kafin a karkare da mahawwarar bainar jama’a, sannan a dai gefe wannan buki lokaci ne na baje kolin litattafan Hausa.

Tun a karshen shekarun 1960 zuwa farkon shekaru 1970 ne Nijar ta fara gwajin karatun yaki da jahilci don ilmatar da wadanda ba su sami shiga boko ba a lokacin da suke yara kanana. Hausa na daga cikin harsunan da wannan shiri ya shafa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG