Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ramaphosa Ya Yi Tir Da Harin Nuna Tsana A Kasarsa


Shugaba Cyril Ramaphosa
Shugaba Cyril Ramaphosa

Shugaban Afirka ta Kudu, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai akan ‘yan kasashen waje da wuraren harkokin kasuwancinsu a sassan biranen Johannesburg da Pretoria, ya na mai cewa ba za su lamunta da lamarin ba.

“Sam kasarmu ba ta goyon bayan nuna kyama ga wani,“ in ji Shugaba Cyril Ramaphosa, a wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, yana mai cewa, “ba za mu amince a rika kai hari akan jama’ar wasu kasashen Afirka ba.”

Ya kara da cewa, “ba hujja ba ce ga mutanensu su rika kai hari akan wasu mutane da wuraren kasuwancinsu, don su na zargin ‘yan wasu kasashe sun mamaye ayyukan yi a kasar.

Darren Taylor, wakilin Muryar Amurka a birnin na Johannaburg, ya ce bisa abin da ya lura da shi, da kuma duk kwararrun da ya zanta da su, bai yarda cewa ‘yan kasashen waje sun mamaye ayyukan a Afirka ta Kudu ba, hasali ma, su ne suke samar da ayyukan yi ga kasar.

An dai kwashe kwanaki uku kenan, wasu ‘yan Afirka ta Kudu su na kai hari akan ‘yan kasashen waje da suka fito daga Najeriya, Ghana da sauran kasashen nahiyar Afirka, saboda a cewarsu sun yi babakere a harkokin kasuwancin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG