Magoya bayan shugaban 'yan adawar Kenya, Raila Odinga, kusan 1,000 ne su ka taru daura da hanyar jirgin kasa da ke unguwar marasa galihu ta Kibera a Nairobi,babban birnin kasa a jiya Lahadi don sauraron jawabinsa, bayan galabar da abokin karawarsa, Uhuru Kenyatta ya yi kansa a zazzafan zaben Shugaban kasa da aka yi kwanan nan.
Amma Odinga da sauran mambobin kungiyar gamayyarsu ta NASA sun ce sace nasarar aka yi daga wurinsu, matsayin da su ka yi ta jaddadawa kenan ga magoya bayansu da ke cike da zakuwa.
Ya ce, "Mun zo nan ne don mu ce ku yi hakuri, ku yi hakuri, ku yi hakuri da abin da ya faru anan wurin jiya da kuma waccen ranar," a cewar Odinga.
Ya kuma kara da cewa, "Su na so su sace nasararmu, sannan kuma sun zo su kashe jama'armu. Wannan shi ake kira rashin bin doka."
To sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Kenya Manoah Esipisu ya karyata wadannan zarge-zargen.
"Shugaban kasa ya ci wannan zaben kiri-kiri, masu saka ido da gida da na waje duk sun tabbatar da hakan," a cewar Esipisu.
Ya kara da cewa, mutane irinsu tsohon sakararen harkokin wajen Amurka John Kerry da Shugaba Thabo Mbeki na Afirka Ta Kudu, wadanda duk suka ce an yi zaben cikin adalci.
Facebook Forum