Cibiyar ta kula da bakin haure ta MDD ta ce hasali alkalumanta basu ma kai cikakken adadin wadanda abin kan rutsa da su ba saboda ba duk lokacin da bakin haure su ka mutu akan ba da rahoton ba, kuma wasu ma ba a taba gano gawarwakinsu. Duk da haka ma lura da al’amura sun ce alkaluman na nuni da irin irin hadarin da ke jiran ‘yan gudun hijira da bakin hauren da ke daukar kasada a yayin nemar mafaka ko fiyayyar rayuwa.
Rahoton ya nuna cewa mutane kusan 18,000 sun mutu ko kuma sun bace bata tekun Bahar Rum tsakanin tsakanin 2014 da 2018. Rahoton ya ce ba a samu gawarwakin sulusu biyu na adadin wadanda abin ya rutsa da su ba.
Mai magana da yawun IOM, Joel Millman, ya ce ‘yan gudun Rohingya ne su ka fi yawa cikin ‘yan gudun hijira 2,200 da su ka mutu a Kudu maso gabashin Asiya kuma akasarin mutane 288 da su ka mutu kudancin Asiya tun daga 2014 bakin hauren Afghanistan ne.
Millman ya gaya ma Muryar Amurka cewa a Kudin Bayanan IOM na Wadanda su ka bace ana wa bakin hauran da su ka bace lakabi da Mutanen Da Ke Tafe. Ya ce akwai rukuni daban na wadanda su ka mutu a hannun hukumomi, kodaye wani sa’in akan samu akasi.
Ya ce an shigar da bayanan wasu bakin hauren da su ka mutu kasa da sa’o’i biyu da shigarsu hannun hukumomi a kudin bayanai na Komfuta na yanzu.
Wani rahoto mai alaka da wannan da kungiyar ta IOM da Asusun Kula da Yara na MDD su ka fitar kwanan nan, ya fi mai da hankali ne kan karuwar yawan yaran da ke shiga sahun bakin haure mai cike da hadari. Alkaluma sun nuna yara kusan 1,600, wato wajen guda a kowace rana, aka samu rahoton mutuwarsu ko bacewarsu tsakanin 2014 da 2018. Kwararru sun kara da cewa ba a ma san cikakken tsananin wannan bala’in ba saboda da yawa daga cikin irin wadanda yaran su kan mutu ba tare da an samu rahoto ba.
Facebook Forum