Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin 'Yan Najeriya Kan Shiga Kungiyar BRICS


Wani taron kasashen BRICS a Rasha
Wani taron kasashen BRICS a Rasha

Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Waje ta fitar mai dauke da sa hannun Mukaddashin mai magana da yawun ta, Kimiebi Imomotimi ta ce Najeriya ta zama kasa ta 9 da ta shiga Kungiyar BRICS a matsayin Kasa amintacciya da ta karbi goron gayyata domin hadin gwiwa da Kungiyar..

Amma tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje Bolaji Akinyemi ya soki wannan mataki a daidai lokacin da wani masanin tattalin arziki ke ganin an dauki matakin dawo wa Najeriya da martabar ta ne.

Wannan Kungiya da aka fi sani da BRICS, Kungiya ce ta manyan kasashe masu tasowa da suke ba wa junan su wani dandali na musamman don habbaka Kasuwanci, saka hannun jari da hadin gwiwar zamantakewa da tattalin arziki tsakanin kasashen da ke membobin Kungiyar.

Najeriya ita ce kasa ta 9 da ta amsa goron gaiyatar shiga Kungiyar a matsayin daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka.

Sauran Kasashen su ne Belarus,Bolivia,Cuba,Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekhistan, wadannan Kasashe 9 na Kawance ne na hadin gwiwa. Sannan akwai kasashe da suke mambobin Kungiyar irin su Brazil, India, Sin (China) da Afirka ta Kudu.

To mene ne Najeriya za ta amfana a matsayin kawa ga kungiyar, Masanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati ya yi nazari cewa akwai maganar siyasa ta Duniya da zai amfani Kasar idan ana tafiya da irin su kasar Sin mai ababe dayawa kama daga kimiya da fasaha, noma, da dukanin fanonin rayuwa da za a amfana da su. Saidai Mikati ya ce maimakon a ce muna kawance da Kungiyar, da gara a ce mu mamba ne, da zai fi alfanu.

Ko akwai alfanu a dangantakar kasashen BRICS ko babu dai, shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa kasashen da ke kungiyar barazan cewa zasu biya haraji kashi 100 cikin 100 a duk wani kasuwanci da ya hada su da Kasar Amurka, wani abu da mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya Abdulazeez Abdulazeez ya yi tsokaci akai yana cewa wannan barazana ba zai shafi dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka ba domin Najeriya ba mamba ce a kungiyar BRICS ba, kawa ce kawai.

Abdulazeez ya ce Najeriya ita ce Kasa mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka wanda ya sa kasashe suna rige rigen hulda da ita. Saboda haka Najeriya ta karbi wannan gaiyata ne domin ta bunkasa tattalin arzikin ta da karfafa dagantaka da wasu kasashe.

A wata hira da ya yi da gidan telebijin na Channels, tsohon Ministan Harkokin Waje Forfesa Bolaji Akinyemi ya yi tir da amsa gaiyatar da Najeriya ta yi na zama kawa ga Kungiyar BRICS maimakon ta yi kokari domin ta zama mamba.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

 Ra’ayoyi Akan Zaman Najeriya Kasa Ta 9 Da Ta Shiga Kungiyar BRICS.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG