Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi A Jihohin Delta Da Adamawa


Taron PDP
Taron PDP

Zabubbukan zuwa ne bayan da Kotun Koli ta bada ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi, inda ta umarci gwamnatin tarayya ta biya kaso 20.60 cikin 100 na kason kudaden kananan hukumomin zuwa asusun ajiyarsu kai tsaye kuma ba cikin asusun ajiyar da gwamnoni ke juyawa ba.

Jam’iyyar PDP ta lashe ilahirin kujerun kananan hukumomin jihar Adamawa 21 a zaben da aka kammala a baya-bayan nan.

A cewar sakamakon zaben da hukumar zaben jihar ta saki, PDP din ta kuma lashe ilahirin kujerun kansiloli a mazabu 226 a jihar dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya, in banda a mazabar Demsa dake karamar hukumar Demsa inda jam’iyyar NNPP ta lashe kujerar kansila guda.

Shugaban hukumar zaben, Muhammad Umar, ya bayyana cewar jam’iyyar mai mulki ta samu nasara da gagarumin rinjaye a ilahirin kananan hukumomin jihar 21.

Ya bayyana sakamakon zaben ne da yammacin jiya Lahadi a shelkwatar hukumar dake Yola, babban birnin jihar.

A cewar Umar, daga cikin jam’iyyun siyasa 19 dake da rijista a jihar, 12 ne suka shiga zaben.

A wani labarin mai nasaba da wannan kuma, haka al’amarin ya kasance a Delta inda jam’iyyar PDP tayi nasara a ilahirin kananan hukumomin jihar 25 inda ta lashe kujerun ciyamomi a zaben daya gudana a ranar Asabar, 13 ga watan Yulin da muke ciki.

A jiya Lahadi, Shugaban hukumar zaben jihar Delta, Jerry Agbaike, ya bayyana cewar daya daga cikin ‘yan takarar pdp ya lashe zaben ba tare da hamayya ba.
‘Yan takarar PDP sun fafata da sauran jam’iyyu kuma sun samu galaba a kananan hukumomi 24 da aka gudanar da zaben.

Sai dai, zaben bai gudana a karamar hukumar Udu ba kasancewar an zabi dan takarar jam’iyyar PDP, Vincent Oyibode, ba tare da hamayya ba.

Haka kuma, ‘yan takarar kansila sun fafata tare da yin galaba a mazabu 499 dake fadin jihar yayin da jam’iyyar APM ta lashe kujerar kansila daya tilo a wata mazaba dake karamar hukumar Shimili ta Arewa dake jihar.

Zabubbukan 2 na zuwa ne bayan da Kotun Koli ta bada ‘yancin cin gashin kan tasirifi da kudade ga kananan hukumomi, inda ta umarci gwamnatin tarayya ta biya kaso 20.60 cikin 100 na kason kudaden kananan hukumomin kasar nan 774 zuwa asusun ajiyarsu kai tsaye kuma ba cikin asusun ajiyar da gwamnoni ke juyawa ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG