Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2027 – Atiku Abubakar


Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Alhaji Atiku, wadda karo na biyar kenan da ya tsaya takarar shugaban kasar bayan dawowar Najeriya dimokraddiya a shekarar 1999, a zaben da aka gudanar a shekarar 2023, ya ce “insha Allahu” da aka yi masa tambayar ko zai tsaya takara a zaben 2027.

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa kuma Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya tabattar wa Muryar Amurka cewa zai tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2027 duk da kalubaloli da jam’iyyarsa ta PDP ke fuskanta a yanzu haka.

Alhaji Atiku ya tabattar da hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, a Abuja, birnin tarayyar Najeriya.

Alhaji Atiku, wadda karo na biyar kenan da ya tsaya takarar shugaban kasar bayan dawowar Najeriya dimokraddiya a shekarar 1999, a zaben da aka gudanar a shekarar 2023, ya ce “insha Allahu” da aka yi masa tambayar ko zai tsaya takara a zaben 2027.

Ya kara da cewa ba zai ja da baya ba a tsayawa takarar shugaban kasa har tsawon “iyakacin lokacin da Allah ya bani karfi ko lafiya da kuma yawan rai”.

(daga hannun hagu) Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha da Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar
(daga hannun hagu) Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha da Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma amince cewa ya wajabta jam’iyyar PDP ta hada gwiwa da wasu jam’iyyu idan har za ta kwato ragamar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai ci.

“A yadda jam’iyyar PDP ta ke a yanzu, idan ta tsaya zabe, babu yadda za ta yi ta samu nasara. Ta na bukatar hadin gwiwa da wasu jam’i’yoyyi”.

Alhaji Atiku Abubakar dai ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a lokuta daban daban so shida, in da ya fafata, kuma bai yi nasara ba a zaben fidda gwani, da marigayi MKO Abiola da Babagana Kingibe yayin neman tikitin jam’iyyar SDP a shekarar 1993, kana ya tsaya a shekarar 2007 a jam’iyyar ACN, 2011 a jam’iyyar PDP, 2015 a jam’iyyar APC, 2019 a jam’iyyar PDP da 2023 a jam’iyyar PDP inda duk lokutan ya samu tikiti amma bai yi nasara ba a zabubbukan da suka gudana.

Alhaji Atiku ya kuma nanata alkawalin da yi a shekarar 2003 na marawa duk wanda jam’iyyarsa ta baiwa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa saboda “idan har abunda ya fi wa jam’iyya kyau kenan, sai mu bi a jam’iyyance. Na tabatta jam’iyya za ta yi abun da zai fi ma Najeriya kyau kuma zai yi wa jam’iyya kyau”, in ji shi

Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2027 –Atiku Abubakar
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

‘Rashin hadin kai’

Yayin da Najeriya, musamman arewacin kasar, ke fama da matsaloli iri-iri, Alhaji Atiku yace rashin hadin kai ne ya jefa yankin a halin da ta ke ciki yanzu.

Shahararren dan siyasan ya ce “arewa yanzu ta na jin jiki don rashin hadin kai da ta yi. Rashin hadin kai ya jawo mata yanayin da take ciki yanzu. Akwai rashin zaman lafiya, akwai talauci, kuma rayuwa ya zama wani abu daban" a cewarsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG