Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Lashe Akasarin Kujerun Kananan Hukumomi A Filato


Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, Mr. Plangji Cishak ya ce ya gamsu da yadda zaben ya gudana.

Jami'iyyar PDP mai mulki a jihar Filato ta lashe akasarin kujerun shugabannin kananan hukumomi a zaben da aka gudanar a ranar Laraban da ta gabata.

Jami'iyyu 11 ne suka shiga zaben wanda 'yan takara 75 suka fafata a kujerun ciyamomin kananan hukumomi 17 a jihar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, Mr. Plangji Cishak ya ce ya gamsu da yadda zaben ya gudana.

Duk da yake an kammala zabubbukan ba tare da samun yamutsi ba, Honarabul Kabiru Iliyasu, tsohon kansila a Mangu ward One ya ce wani matashi ya rasa ransa a wurin tattara kuri'u.

Al'ummar jihar Filato dai sun bayyana fatar wadanda suka dare karagar mulkin kananan hukumomin za su magance matsalolin da suke fuskanta da samar musu da ababen more rayuwa.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ana dakon sakamako daga kananan hukumomin Pankshin da Langtang ta Arewa.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos:

PDP Ta Lashe Akasarin Kujerun Kananan Hukumomi A Filato.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG