Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP ta Cacaki APC Kan Zaben Kananan Hukumomin Yobe


Kwanan nan jihar Yobe dake karkashin dokar ta baci inda aka ce ba za'a iya shirya zabe ba amma ta yi wanda kuma PDP ta kauracewa

Jam'iyyar PDP da ta kauracewa zaben kananan hukumomi a jihar Yobe ta cacaki APC kan zaben.

Dr. Yarima Lawal Ngama karamin minista a ma'aikatar kudi ya ce rashin shiga jam'iyyar PDP zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Yobe shi ne mafi a'ala domin kare lafiyar jama'a. Yayin da yake magana da manema labarai ya ce nadi aka yi a jihar tasu ba zabe ba. Ya ce sabili da lalacewar harakar tsaro a jihar wuraren Gulen ba'a hawan mota ko babur domin ma ba'a sayar da man fetur. Ya ce shi kansa ya aika da fiye da kekuna dari da hamsin makon da ya wuce zuwa yankin, Ya ce babu wani zabe da aka yi.An dai dangwala hannu an kammala nadi. Ya ce inda sun shiga aka yi masu wani abu da ance su ne basa son zaman lafiya. Ya ce gwamnan ba sai ya shirya zabe ba. Idan yana so yana iya nada kantamomi. Mutane basu fito ba kowa ya zauna gidansa lamarin da ya nuna jama'a basu da bangaskiya ga gwamnan ko gwamnatinsa.

Da yake mayarda martani kakakin gwamnatin Yobe Abdullahi Bego ya ce tabbas zabe aka yi. In ji shi masu sa ido daga jihohi goma sha biyar suka kalli yadda aka yi zaben. Ban dasu akwai yan jarida da wasu masu zaman kansu duk sun sa ido. Sun ga yadda aka yi zaben cikin lumana da kwanciyar hankali. Ya ce mutane sun fito sun yi cincirindo sun bi layi sun yi zabe. Inda jam'iyyar Ngama ta shiga zaben ta kuma yi korafi to da sun duba.

Dangane da zaben 2015 Dr Ngama ya ce APC zata nade komatsanta ta fice daga Damaturu. Babu abun da APC zata yi a zabe mai zuwa. Inda haka ne a wannan zaben ma'aikata da wadanda suka kauracewa jihar da sun koma gida sun yi zabe amma basu je ba. Kafin nan da 2015 za'a samu zaman lafiya domin kokarin da gwamnatin tarayya take yi ke nan. Ya ce su ANPP suke gani a APC wadda ba komi ba ce ila kwakwacam ce. Ya kara da cewa yadda suka kasa yin mulki shi ya kawo rikicin Borno da Yobe.

Ahmed Bego kakakin gwamnatin Yobe ya ce ga fili ga doki. Ya ce Dr Ngama bai san komi ba a siyasa. Dr Ngama ya san tarihin PDP a jihar Yobe. 'Yan PDP kadan da suka saura suna jiransa su nuna masa cewa shi ba komi ba ne. Jam'iyyar PDP a Najeriya yanzu, inji Bego ba komi ba ce balantana wani Ngama a jihar Yobe.

Saleh Shehu Ashaka nada rahoto.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG