Taron ya hada da shugabannin siyasa da na addinai da ma na al'umma ya mayarda hankali ne kan kalubalen rashin tsaro da ma matsalolin siyasa dake addabar kasar.
Kungiyar ta fito fili ta yi kashedi kan kokarin da a keyi na raba kawunan 'yan Najeriya kan addini da kabilanci. Yusuf Yakubu Arigasiyu mataimakin shugaban kungiyar na kasa a bangaren arewacin Najeriya ya ce sun nuna takaicinsu a kan wannan kasar kan rashin tsaro da aiwata zaman lafiya. Ya ce sun damu da zarge-zargen cewa shugabanni na cikin abubuwan dake faruwa.
Wasikar da tsohon shugaban kasa ya rubutawa shugaba mai ci yanzu ta tayarda hankali. Ya ce lokacin da aka jefa bam shekarar 2010 akwai wadanda suka ce su suka yi amma shugaban kasa ya ce ba su ba ne. Kana an je Maiduguri an shiga barikin sojoji an yi barna, ina sojojin suke? Wadannan sun nuna cewa akwai wata matsala a boye. Yanzu kuma an yi zargin cewa shugaban na horas da wasu domin su kashe mutane 1000. Ya ce ya kamata a yi bincike. Idan Obasanjo ne bashi da gaskiya a hukuntashi. Idan kuma Jonathan ne bashi da gaskiya ya kamata a tsigeshi daga shugabanci. Idan ba haka aka yi ba zai kawo tashin hankali.
Ta bakin wanda yake taimakawa shugaban kasa kan sha'anin addinai Barister Tahir Umar Tahir da ya wakilci mataimakin shugaban kasa a wurin bude taron ya ce akwai rashin fahimtar yadda alamura ke tafiya. Ya ce akwai abubuwa wanda rashin fahimtarsu ya haifi wasu. Akwai kuma wasu kurakurai da suka haifi wasu abubuwan. Ya ce ita wannan gwamnatin ta tarar dasu ne a haka saboda haka kokarin da take yi shi ne ta tabatar da an yi adalci tsakanin al'umma ta kuma kawo gyare-gyare yadda kowane addini da kabila an basu hakinsu.
Murtala Faruk Sanyiinna nada karin bayani.