WASHINGTON, DC —
'Yan Golden Eaglets na Najeriya sun doke takwarorinsu na kasar Uruguay a wasan kwata-fainal na gasar cin kofin kwallon nkafar duniya na samari 'yan kasa da shekara 17 da suka yi yau a Sharjah, Hadaddiyar Daular Larabawa.
Dan wasan Najeriya, Taiwo Awoniyi, shi ne ya jefa dukkan kwallayen biyu ma Najeriya, na farko a cikin minti na 18 da fara wasan, na biyun kuma a bayan da aka komo daga hutun rabin lokaci a minti na 79.
A ranar talata, kuma a wasan kusa da na karshe, Najeriya zata gwabza da 'yan wasan kasar Sweden, wadanda su ma suka doke takwarorinsu na kasar Honduras da ci 2 da 1.
A daya wasan na kwata fainal da aka yi tun farko a yau asabar, Argentina ta doke 'yan wasan Cote D'Ivoire da ci 2 da 1. Yanzu ita ma Argentina zata yi wasan kusa da na karshe ranar talata da 'yan kasar Mexico wadanda suka fitar da Brazil a bugun fenariti jiya jumma'a.
Wadanda suka yi nasara a wasannin biyu na ranar talata, zasu gwabza wasan karshe na cin kofin a ranar jumma'a.