Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Ya Ja Kunnuwan Koriya ta Arewa


Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence yayinda ya ziyarci sojojin Amurka dake Koriya ta Kudu
Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence yayinda ya ziyarci sojojin Amurka dake Koriya ta Kudu

Yayin da yake bada misali da harin da Amurka ta kai akan Afghanistan da kuma Syria, Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya ja kunnuwan Koriya ta Arewa, inda yace Shugaban kasar Amurka Donald Trump zaiyi amfani da karfin soja idan ta kama, akan gwamnatin Kin Jong Un idan har barazanar gwajin makamin kare dangi ta cigaba.

Mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara a Koriya ta Kudu a shirin ziyararsa ta kasashe hudu don kara karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da kawayenta da kuma nuna jajircewar ta ga yankin da ake dari dari dashi gami da gina tallafin kasa da kasa domin kara matsawa gwamnatin Kim Jon Un lamba don dakatar da shirye shiryen gwajin makamin kare dangi da kuma na makami mai linzami samfurin Ballistic.

A daya bangaren kuma Alkali a Koriya ta Kudu ya tuhumi tsohuwar shugabar kasar Koriya ta Kudun da aka hambarar daga kan mulki Park Geun-hye da laifin karbar cin hanci lamarin da ya kaiga tsigeta.

Ofishin kotun ya tuhume ta ne a yau Litinin inda aka maida shari’arta zuwa Kotun Munanan Laifuka.

Munanan laifukan da ake tuhumar Park da su sun hada da rikicin da ya jawo ta rasa mukaminta. An zargeta da hada kai da wata tsohuwar kawarta Choi Soon-sil da damfarar wasu kamfanoni su bada gudummawa ta fiye da Dalar Amurka miliyan $69 zuwa wasu Gidauniyoyi guda biyu na jabu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG