Shugaban majalisar zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Turai, Donald Tusk ya bayyana bukatar a karawa Burtaniyya lokaci har zuwa watan Afirilun shekara mai zuwa don ta sami damar fito da kwakkwaran shiri na ballewar ta daga tarayyar ta EU.
Dole ne shugabannin tarayyar Turan su amince da karin lokacin wanda zai ba Burtaniyya damar barin kungiyar kafin cikar wa’adin idan majalisar dokokin kasar ta amince da yarjejeniyar fita daga tarayyar ta EU.
Yau Jumma’a ake sa ran firayin ministar Burtaniyya Theresa May zata rubutawa Tusk wasika a hukumance don neman karin lokacin, har zuwa 30 ga watan Yunin wannan shekara.
Dama ranar 29 ga watan Maris ya kamata Burtaniyya ta bar tarayyar Turan, amma May ta sami amincewa daga EU akan karin lokaci don gwamnatinta ta sami lokacin fito da shawarar da ‘yan majalisar dokokin Burtaniyya zasu goyi baya.
Facebook Forum