Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Hade Yammacin Kogin Jordan Da Isra'ila Idan Na Lashe Zabe - Netanyahu

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanhayu. Ranar Afrilu 1, 2019.
Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanhayu. Ranar Afrilu 1, 2019.

Akwai yiwuwar wannan alkawari da Firai minista Netayahu ya yi, ya harzuka Falasadinawa da sauran kasashen Larabawa, yayin da ake gab da tunkarar zabe a Isra’ilan.

Firai ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce idan ya lashe zaben da ke tafe, zai hade yankunan Yahudawa da yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.

Netanyahu ya bayyana hakan ne, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Channel 12 News.

Akwai yiwuwar wannan alkawari da Firai minista Netayahu ya yi, ya harzuka Falasadinawa da sauran kasashen Larabawa, yayin da ake gab da tunkarar zabe a Isra’ilan.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Isra’ila ba ta mallake yankin na yammacin gabar kogin Jordan ba, kamar yadda ta yi da gabashin birnin Kudus da kuma Tuddan Golan ba tare da amincewar aksarin kasashen duniya ba, Netanyahu ya ce Isra’ila na da shirin yin hakan, kuma tuni an fara tattaunawa kan batun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG