Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Tace Ta Yi Damara Mai Da Martani Ga Harin Soja Daga India


Firai ministan Pakistan, Imran Khan
Firai ministan Pakistan, Imran Khan

Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya yi kashedi a yau Talata cewa kasar sa zata gaggauta mayar da martani ga duk wani harin soja da India zata kawo mata.

Khan ya yi wannan kashedi ne a wani jawabi ta telbijin yayin da ake fama da tankiya tsakanin kasashen biyu masu makaman nukiliya, wanda suke zaman doya da manja, biyo bayan wani mummunar harin kunar bakin wake a kan sojojin India a yankin Kashmir da ake takaddamna akai.

"Yace idan kuna tunanin kai wani hari a kan Pakistan, toh ita Pakistan ba zata yi wata-wata ba, zata mayar da martani ne". Khan yace bamu da wani zabi illa mu mayar da martani ga duk wani hari daga India.

New Delhi dai ta dora laifin kai harin a gundumar Pulwama da ya yi sanadiyar kashe sama da sojojin India arba’in a kan tungar sojojin Pakistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG