Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Dauki Nauyin Taron Shugabannin Leken Asiri Akan Yaki Da Ta'addanci


Shugaban Pakistan Alif Ali Zardari
Shugaban Pakistan Alif Ali Zardari

Taron da Pakistan ta dauki nauyinsa ya samu halartar jami'an leken asiri daga Rasha, Iran da China domin gano yadda kungiyar ISIS take samun gidin zama a kasar Afghanistan

Pakistan ta dauki dawainiyar wani taron da ba safai ake yi, jiya Laraba inda shugabannin hukumomin leken asiri daga Rasha da Iran, da China suka hallara domin su tattauna kan yaki da ta'addanci da kuma hada kai, musamman sun maida hankali ne kan samun gindin zama da kungiyar ISIS take yi a kasar Afghanistan wacce yaki ya daidaita.

Majiyoyin gwamnati a birnin Islamabad sun tabbatarwa MA cewa, mahalarta taron, sun tattauna dalla dalla kan irin matakai na hadin guiwa domin hana magoya bayan kungiyar 'yan ta'addan ta ISIS dake Afghanistan, yin barazana ga iyakokin kasashen hudu.

Taron na ba saban ba, ya kawo shugabannin hukumomin kasashen, wadanda hare haren ta'addanci daga ISIS ya shafe su kai tsaye, kodashike taron bai auna wata kasa ba,kamar yadda watakil za'a kalla," majiyoyin sun jaddada cewa a yunkurin da suke yi na kauda duk wani tunanin cewa, hada kai da Rasha, da China da Iran, na iya zagon kasa ga kokarin da Amurka take yi na daidaita al'amura a Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG