Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Taka Rawa Akan Yarjejeniyar da Afghanistan Da Taliban Suka Cimma


Yan Taliban suna walwala sanadiyar yarjejeniyar da suka cimma
Yan Taliban suna walwala sanadiyar yarjejeniyar da suka cimma

Yarjejeniyar da Pakistan ta taimaka Afghanistan da Taliban suka cimma ta yi sanadiyar gudanar da bikin sallar Eid el Fitr a kasar ta Afghanistan cikin kwanciyar hankali

Pakistan ta taka muhimmiyar rawa a yarjajjeniyar

tsagaita wutar da aka cimma a watan jiya tsakanin Afghanistan da Taliban, da zummar tabbatar da cewa mutanen kasar sun gudanar da bukukuwan karamar Sallah ta Eid el Fitr cikin kwanciyar hankali.

Wannan ya dada inganta dangantakar Pakistan da Afghanistan, wadda ta yi tsami na kusan tsawon shekaru biyu.

Lokacin da aka ba da sanarwar tsagaita wutar, sai wasu mayakan Taliban su ka nufi cikin birane, da dama daga cikinsu su ka yi ta daukar hotuna da mutanen unguwa. Wasunsu kuma su ka yi salla tare da jami'an tsaron gwamnati -- wadanda su ka sha fafatawa da su a baya. Da dama daga cikinsu sun gaya ma manema labarai cewa su fa sun gaji ma da yakin.

To amma wannan tsagaita wuta na wuccin gadi, wanda aka dauka a matsayin wani babban mataki na ganin cewa an yi nasarar sasantawa a Afghanistan, ya kasa yin sanadin wata sabuwar tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a yankin, inda Taliban ta ma ki tayin tsawaita tsagaita wutar da Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG