Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Turkiya Ya Fara Sabon Wa'adin Mulki Da Cikakken Iko


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

A kasar Turkiya shugaban kasa Recep Tayyib Erdogan ya fara sabon wa'adin mulki da cikakken iko lamarin da wasu ke tsoron cewa shugaban na iya rikidewa ya zama mai mulkin kama karya

Shugaban kasar Turkiyya Rajib Tayyib Erdogan, ya fara aiki tareda sabbin karin iko, a dai dai lokacind a kasar take komawa tsarin shugaban kasa mai cikakken iko.

"Nayi alkawarin karfafa hadin kai da dangantaka tsakanin mu," Erdogan, ya fadawa majalisar dokokin kasar jiya Litinin, bayan da yayi rantsuwar kama aiki na wani sabon wa'adi.Wakilai daga jam'iyyarsa ta AKP suna sowa, yayinda 'yan hamayya suna zaune shiru.

'Yan hamayya suna gargadin cewa Turkiyya tana fuskantar shugaba mai salon mulkin kama-karya, wadda jama'a suka zaba. Sai dai shugaba Erdogan ya dage cewa dumbin iko da ya samu a yanzu suna da muhimmanci domin tunkarar kalubale na rarrabuwar kawuna ta siyasa da kasar take fuskanta.

An kama daliban kasar 6 ranar Jumma'a, abikin saukar karatu saboda sun rike katon zane na ba'a ga shugaba Erdogan. Dukkan su suna fuskantar zargin zagin shugaban kasa. Wasu masu nazarin al'amuran yau da kullum suna jin shugaba Erdogan yana iya amfani da dumbin ikon da yake dashi ya magance matsalar rarrabuwar kawuna da kasar take fama dashi. Firai Ministan kasar mai barin gado Binali Yildrim ya nuna alamun cewa da shugaba Erdogan zai kawo karshen aiki da dokar ta baci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG