A Pakistan, ministan harkokin cikin gidan kasar Chaudry Nisar Ali khan, yace gwamnati tana da bayanai cewa 'yan ta'adda suna kimtsa wani hari shigen irin mummunar harin nan da suka kai kan wata makarantar soja, cikin makon jiya.
Khan bai bada wani karin bayani ba, amma yace tilas 'yan kasar baki daya suka kwana cikin shiri. Ya gargadi kamfanonin wayoyin celula cewa zasu fuskanci tuhumar ta'adanci muddin suka bada shaidar bogi ta mallakar lambobin wayar tarho.
Haka nan kuma minista Khan ya gayawa masu O'tel O'tel cewa su tabbatar da shaidar baki da suke baiwa masauki, yace za'a aza musu laiifi, muddin suka baiwa 'yan ta'adda masauki. Yayi kira ga al'ummar kasar baki daya su baiwa jami'an tsaro hadin kai ta wajen basu duk wani bayani da suke da shi da zai taimaka su tabbatar da zaman lafiya.
Ministan harkokin cikin gidan yace rundunar sojojin kasar tana iya kaddamar da hari na gama gari kan birane inda 'yan ta'adda suke da zama, amma tana gudun daukan matakin saboda kada ya rutsa da fararen hula. Yace sojojin kasar basa auna hari kan mata da kuma yara.
A cikin makon jiya ne 'yan bindiga na kungiyar Taliban dake kasar, suka kai farmaki kan wata makarantar da rundunar sojojin kasar take lura da ita a Peshwar, suka kashe kusan dalibai 150 da kuma malamai.
Kungiyar Taliban din ta kira harin ramuwar gayya kan hare haren da sojojin kasar suke kaiwa kan mayakan sakai din.