Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Wasu 'Yan Kwadago a Pakistan


Sojojin Pakistan.
Sojojin Pakistan.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana a kudu maso yammacin kasar Pakistan, wasu 'yan bindiga sun harbe wasu leburori, wato 'yan kwadago 7 har lahira.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana a kudu maso yammacin kasar Pakistan, wasu 'yan bindiga sun harbe wasu leburori, wato 'yan kwadago 7 har lahira.

Hukumomin sun ce wadanda aka kashen, 'yan Lardin Punjab ne a gabashin kasar, kuma sace su aka yi daga wata gonar noman kaji a yankin Baluchistan mai fama da tashin tashina.

Shekara da shekaru kenan da Baluchistan ke fama da boren 'yan aware. Kungiyoyin masu kishin yankin Baluchistan mai fama da fatara da talauci, sun dade su na zargin gwamnatin tarayya da kwashe arzikin karkashin kasar yankin, amma ba ta damu da tsananin wahalar da jama'ar yankin ke sha ba.

'Yan tawayen sun saba kai hare-hare kan jami'an tsaro, da gine-ginen gwamnati da kuma fararen hula a Baluchistan, kuma su kan kai hari kan sauran kabilun kasar Pakistan da suka yi kaka gida a Lardin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG