Fitattun tagwayen mawakan Najeriya P-Square sun nemi masoyansu su yafe musu saboda rabuwa da suka yi na tsawon shekaru.
A shekarar 2017 mawakan suka samu sabani, lamarin da ya kai ga suka bangare – kowa ya kama gabansa.
Rahotanni sun nuna cewa fitattun mutane a Najeriya da dama ciki har da masu mulki sun yi yunkuri shirya su amma abin ya ci tura.
Sai dai bayan sulhu da suka yi a ‘yan watannin bayan nan, a karon farko mawakan biyu sun gudanar da wasa tare.
Rabon da su yi waka tare tun kusan shekaru biyar da suka gabata.
Yayin wasan kalankuwar da aka shirya a lokacin bukukuwan Kirsimeti a birnin Legas a karshen makon da ya gabata, mawakan sun nemi afuwar masoyansu a duk fadin duniya, inda har suka durkusa da gwiwowinsu.
“Muna masu ba ku hakuri bisa rabuwa da muka yi, muna so kowa a duk fadin duniya ya san cewa muna neman afuwa.” P-Square suke ce.
A kwanan tagwayen, wadanda ‘yan asalin birnin Jos ne da ke jihar Filato, suka yi bikin cika shekara 40 da haihuwa.