Jam’iyyar gwamnati APC ta sanar da dage babban taron ta na zaben sabbin shugabanni da tsawon wata daya daga ranar da a ka tsara gudanar da taron a 26 ga watan nan.
Yanzu jam’iyyar ta ce za ta gudanar da taron a ranar 26 ga watan gobe.
Bayan taron masu ruwa da tsaki APC karkashin Mai Mala Buni ta ce za ta yi amfani da ranar 26 ga watan nan wajen gudanar da zaben shiyyoyi, duk da ba ta fadi dalilan gaza gudanar da wadannan taruka ba.
A hirar shi da Muryar Amurka, Salisu Na'inna Dambatta daraktan yadda labarai na jam'iyyar APC ya ce za a yi amfani da ranaku gabanin babban taron wajen tantance ‘yan takarar daga shiyyoyi har ma da karbar korafi don gudanar da taron ba tare da barin baya da kura ba. Daraktan ya kara da cewa ba wata tababa game da sabuwar ranar
Tuni a ka fara samun martani tsakanin masu ganin a jira zuwa wani lokaci, da masu cewa ba su da kwarin guiwar ba za a sake dagewa daga sabuwar ranar ba.
Jam’iyyar APC da ta faro mulki daga shekara ta 2015 na fafutukar neman zarcewa da mulki idan shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya kammala wa’adi a 2023.
Baya ga babbar jam’iyyar adawa PDP da a baya ta yi mulki na tsawon shekaru 16, akwai bayanan da ke nuna manyan ‘yan siyasa da ba su gamsu da tafiyar manyan jam’iyyun biyu ba, na shirin kafa sabuwar jam’iyya don neman amsar ragamar mulki a zaben mai zuwa.
An dai dade ana kai ruwa rana kan batun shirya baban taron jam’iyyar mai mulki wanda a da, aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2022, amma batutuwan da suka hada da tsarin raba kujeru zuwa shiyya-shiyya da rikice-rikice da aka fuskanta a jam’iyyar APC a matakin jihohin na zama barazana.
Idan ana iya tunawa, wannan ba shi ne karon farko da jam'i da rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa da kulle kulle tsakanin jiga-jigan jam'iyyar ta APC.