Hukumar ta shiga kulla yarjeniyoyin ne domin samun cigaba mai dorewa kamar yadda kasashen suka yi anfani da nasu hukumomin horaswa suka cigaba.
Dr. Joseph Ari yace kasa kamar Israila tanada wata makaranta dake bada koyaswa akan sana'ar noma. Hukumarsa ta ITF ta tura wasu makarantar domin bunkasa noma a Najeriya.
Kasar Brazil ma tana da wata makaranta haka kwatankwacin ITF kuma tayi suna wajen horas da ma'aikata sana'o'i daban daban kuma ba'a maganar cigaba a cikin Brazil ba'a ambaci makarantar ba. Sunyi yarjejeniya da makarantar domin su samu abun da zasu koyas a Najeriya.
A kasar Singapor ma akwai ITE wadda tare da hadin gwuiwarta suka kafa wata makaranta a Abuja inda yanzu suna koyas da sana'o'in hannu har guda biyar.
To saidai a Najeriya daliban manyan makarantu ne suka fi cin gajiyar ITF inda suke samun horo da sanin makaman aiki.
Amma daraktan na ITF yace baicin daliban jami'o'i yanzu suna maida hankali kan sauran matasan Najeriya saboda, injishi aikin hannu shi zai sa kasar Najeriya ta cigaba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.