Wasu ‘yan bindiga sun kai harin kan wani ayarin motocin Ofishin Jakadancin Amurka a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Harin wanda aka kai a ranar Talata, ya yi sanadin mutuwar jami'an ofishin jakadancin Amurka biyu da ‘yan sanda biyu a cewar rundunar ‘yan sandan jihar.
“An kai hari kan ayarin motocin Amurka, amma babu Ba’amurke a tafiyar, saboda haka, babu wani Ba’amurke da aka jikkata, amma muna da labarin cewa rasa rai.” Kakakin Majalisar Tsaron Amurka John Kirby ya fada a taron manema labarai a Fadar White House a ranar Talata.
Bayanai sun yi nuni da cewa, wadanda suka rasa rayukansu, ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka ne 'yan Najeriya muna kuma gudanar da bincike tare da hadin gwiwar jami'an tsaron kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun bude wuta ne akan ayarin motocin na ofishin jakadancin Amurka, a daidai hanyar karamar hukumar Ogbaru da ke jihar.
Anambra na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan aware a kudancin Najeriya.
“‘Yan bindigar sun kashe ‘yan sanda biyu da kuma wasu jami’an Karamin Ofishin Jakadancin Amurka biyu, sun kuma cinnawa gawarwakinsu da motocinsu wuta.” Kakakin ‘yan sandan jihar Anambra Tochukwu Ikenga ya ce.
Jim kadan bayan harin, an tura jami’an tsaro, amma ba su tarar da maharan ba, wadanda har ila yau suka yi garkuwa da wasu ‘yan sanda biyu da kuma direban daya daga cikin motocin tawagar.
Ikenga ya kara jaddada cewa babu dan kasar Amurka cikin mutanen da ke ayarin motocin jami’an ofishin jakadancin na Amurka.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce jami’anta na aiki tare da jami’an tsaron Najeriya don gudanar da bincike kan harin.
“Tsaron lafiyar ma’aikatanmu shi ne abu mafi muhimmanci a gare mu, muna kuma daukan kwararan matakan kariya idan muka shirya irin wannan tafiya,” Sanarwar ta Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kara da cewa.
Babu dai cikakken bayani kan inda ayarin motocin jami’an ofishin jakadancin na Amurk ya nufa a jihar ta Anambra, kuma ba a san iya adadin mutanen da ke ciki ba a cewar AP.