Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani Kan Sabon Kudirin Tsarin Haraji A Najeriya


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Kudirin sabon fasalin gyara tsarin haraji da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kudura aiwatarwa a Najeriya, ya janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar, musamman masu ruwa da tsaki da ma 'yan kasuwa.

Gwamnatin Najeriya ta ce, kudirin tsarin harajin na shekara ta dubu biyu da ishirin da hudu, zai magance rudanin da ke tattare da tsarin tattara kudaden haraji da ya dade a kasar, ta hanyar karfafa dangantaka tsakanin gwamnati da masu biyan haraji.

Mai fashin baki kan lamuran yau da kullum, Mr Japhet Philip, ya bayyana yadda sabon tsarin harajin zai kasance.

"Al'fanun sabon tsarin harajin shi ne samun karuwar kudin shiga, kuma kamfanonin da suke kaucewa biyan haraji dokar za ta tilasta musu biya kuma zai yi maganin biyan haraji barkatai da jama'a ke yi," a cewar Mr. Philip.

Ya kara da cewa, "Matsalar tsarin shi ne nan gaba kudaden shiga na VAT zasu shiga asusun gwamnatin tarayya ne kadai, jihohi da kananan hukumomi ba zasu amfana ba."

Wata majiya ta ce gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana bukatar sake duba wasu bangarorin sabon kudurin tsarin harajin.

Gwamnan na jihar Nasarawa, wanda rahotanni suka bayyana cewa yayi wannan maganar ne da yawun sauran gwamnonin jihohin Arewa, ya ce ba wai suna kin amincewa da sabon tsarin bane sai dai suna bukatar a sake duba batun cire harajin VAT don kaucewa rashin fa'idarsa ga yankin Arewa.

A bangare guda kuwa, a wata sanarwa daga kungiyar Yarbawa ta Afenifere, a ta bakin jami'inta Jare Ajayi, ya bayyana cewa, rabon kason ribar da aka samu ta hanyar VAT ba zai kasance da matsala ba, don haka kar wani bangaren kasar ya yi fargaba.

Sakataren hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwa ta Arewacin Najeriya, Alhaji Bashiru Uba Hassan, ya ce haraji na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa, amma akwai bukatar gwamnati ta sake fasalin sabon tsarin nata.

"Inda muke bukatar gwamnati ta yi gyara shi ne yadda kudurin ya ce jihohin da ke da kamfanoni su ne zasu sami kaso mai yawa daga kudin shiga, yayin da wasu jihohi zasu tashi ba komai."

Saurari rahoton Zainab Babaji:

Martani Kan Sabon Kudirin Tsarin Haraji A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG