WASHINGTON D.C. —
A cikin shirin noma tushen arziki na wannan makon, za mu daura a inda muka tsaya a makon jiya, a tataunawa da Darektan Ma’aikatar Gidan Gona na jihar Agadas da ke jamhuriyar Nijar, Mahamane Ma’azu Umaru Sanda, kan matsalar karanci ruwan sama da aka fuskanta a daminar bana da kwararowar hamada da kuma kwari, wanda ya sa da yawa daga cikin manoma kauracewa gonakinsu, inda masana ke hasashen cewa za’a iya fuskantar karanci abinci.