Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NOMA: Gwamnatin Jihar Benue Ta Yi Karin Hutun Karshen Mako Ga Ma'aikata


Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.

Gwamnatin jihar Benue ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a na kowane sati a cikin watannin Yuni da Yuli, a matsayin ranakun hutu ga ma’aikatan gwamnati, domin baiwa ma’aikatan damar fuskantar aikin gona.

A cikin wata sanarwar umarni da babban sakatare Sir. Samuel Udeh ya fitar a madadin shugaban ma’aikatan jihar, gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce an dauki wannan matakin ne domin bai wa ma’aikatan gwamnatin jihar damar morewa fa’idar da jihar ta ke da shi na albarkar noma.

Ranakun hutun za su soma aiki ne daga Alhamis, 17 ga watannan nan na Yuni, har zuwa Juma’a 30 ga watan Yulin shekarar nan ta 2021.

To sai dai hutun bai shafi masu muhimman ayukan bukatun jama’a, kamar ma’aikatan lafiya da ire-iren su ba.

Matakin a cewar gwamnan, ya zo ne daidai da kudurin gwamnatin jihar na bunkasa sha’anin aikin gona a jihar.

Akan haka yayi kira ga dukan ma’aikata a jihar da su yi cikakken amfani da wannan dama,wajen ba da tasu gudummuwa ta haujin bunkasa noman kayayyakin abinci har ma da na sayarwa, musamman a wannan lokaci da Najeriya ta ke da matukar bukatar farfado da aikin gona.

Wannan matakin na gwamnati na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar jihar da ma sauran sassan Arewacin Najeriya suke fatan daidaituwar al’amura, bayan kwashe kusan shekaru 2 ba’a sami damar yin noma a wasu sassa ba saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.

A can baya dai an sami rahotannin da dama na kai farmaki tare da kisan manoma a lokacin da suke aiki a gonakinsu, wadanda ake ta’allakawa da kungiyar Boko Haram musamman a jihar Borno, yayin da a jihohin Benue, Naija, Katsina, Zamfara da Sokoto kuma, manoma da dama suka kauracewa gonakinsu, sakamakon fargabar hare-haren ‘yan bindiga.

Wadannan matsalolin kuma sun zo daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta dauki matakan rufe kan iyakokin ta da hana shigowa da kayan abinci, tare da zimmar mai da hankali wajen bunkasa sha’anin noma a cikin gida.

XS
SM
MD
LG