Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Bukaci Gwamnati Da Ta Gaggauta Ceto Daliban Islamiyyar Tegina


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

‘Yan majalisar sun ce yanzu makwanni 2 ke nan da aka sace daliban, kuma har kawo yanzu suna can hannun ‘yan bindiga.

Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta hada hannu da gwamnatin jihar Naija, domin ganin an kubutar da daliban makarantar Islamiyya ta Salisu Tanko.

Haka kuma majalisar ta nemi gwamnati da ta kara kaimi wajen inganta sha’anin tsaro a fadin kasar domin shawo kan kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Hakan ko ya biyo ne bayan wani kuduri da ‘yan majalisar wakilan daga jihar Naija, Saidu Musa Abdullahi, Abdullahi Garba, Mohammed Bago, Abubakar Suleja, Mamudu Abdullahi, Jafaru Mohammed, Barwa Beji, Usman Abdullahi, Saidu Doka da Salihu Salleh suka gabatar a zauren majalisar.

Kudurin mai taken “Bukatar gaggawa ta ceto dalibai 136 da aka sace a Tegina da ke cikin karamar hukumar mulkin Rafi a jihar Naija,” ya kuma sami goyon baya da amincewar daukacin majalisar wakilan baki daya.

‘Yan majalisar sun ce yanzu makwanni 2 ke nan da aka sace daliban, kuma har kawo yanzu suna can hannun ‘yan bindiga.

Haka kuma sun bayyana damuwa akan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da cin karensu ba babbaka, ta hanyar “azabtarwa da kisan jama’ar da basu ji ba basu gani ba, lalata dukiyoyi da gidaje, sace abinci da dabbobi da kuma cusa fargabar da tsoro a zukatan al’umma a cikin jihar da ma duk fadin Najeriya.”

Majalisar wakilan ta kuma bayyana bacin rai akan yadda kokarin gwamnatoci ta haujin bunkasa sha’anin noma ya ke kokarin tashi a tutar babu, a yayin da manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda fargabar hare-haren ‘yan ta’adda.

Wannan kuwa a cewar majalisar, kan iya haifar da matsalar karancin abinci, tare kuma da yin barazana ga zaman lafiya da zamantakewar jama’a ta bangaren tattalin arziki, muddin ba’a dauki kwakkwaran mataki ba.

Da yammacin ranar 30 ga watan Mayun nan da ya shige ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko a garin Tegina da ke cikin karamar hukumar mulkin Rafi a jihar Naija, inda suka yi awon gaba da dalibai fiye da 100.

Rahotanni sun bayyana cewa yaran da aka sace dai kanana ne, akasari daga ‘yan shekaru 3 zuwa 14.

‘Yan bindigar sun sako 7 daga cikin daliban saboda karancin shekaru, a yayin da kuma aka ba da rahoton cewa an sami gawar yaro daya da ya mutu a hannun ‘yan bindigar.

Haka kuma lamarin ya jefa wasu iyayen yaran a cikin mawuyacin hali na rayuwa da lafiyar jikinsu.

XS
SM
MD
LG